23 Yuni 2025 - 18:51
Source: ABNA24
Jiragen Dakon Man Ƙasashen Turai Suna Tsoron Shiga Mashigar Hormuz

Jiragen ruwa masu dakon mai suna tsoron tsoron ficewa ta shiga mashigar Hormuz, yayin da kasashen yamma ke tsoron matakin da Iran ta dauka na rufe mashigar Hormuz.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlulbayt (AS) - ABNA - ya habarta cewa: Duba da abubuwan da ke faruwa a wannan yanki tare da bibiyar sabbin labarai da suwk shigow. A cewar shafin Marina Traffic, jirage 54 suka dakata gab da mashigin Hormuz, wanda iya jiragen 2 ne suke yunkurin wucewa mashigilar bisa tsoron faruwar wani abu bayan Iran ta dakatar tare da hana shige da fice a mashigar.

Kafar Sadarwa ta Aljazeera ta fitar da wani faifan bidiyo tana mai nuna irin yadda wannan waje yake mai matukart muhimancin ga kasuwancin kasashen duniya da kuma irin yadda Iranb ta ke da karfi wajen kare shi da ikonta wanda masana suke ganin matukar dai Amurka ta shiga yaki da Iran to Iran zata iya rufe shi kuma hakan zai illata harkar kasuwanci a Duniya gaba daya musammam safarar dan yan mai da sauran kayan masarufi na duniya gaba daya.

Your Comment

You are replying to: .
captcha